Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kungiyar ta kuma sanar da nada sabon shugaba mai suna Abou Hassan al-Hachimi al-Qourachi, kamar yadda kakakin kungiyar Abou Omar al-Mouhajir, ya sanar a wani faifan bidiyo ta hanyar manhajar Telegram ranar Alhamis.
Kungiyar dai bata yi bayyani dalla dalla ba kan sabon shugaban nata wanda shi ne uku tun bayan kafuwarta.
A ranar 3 ga watan Fabarairun da ya gabata ne shugaban Amurka Joe Biden ya sanar cewa shugaban na IS, ya mutu bayan hallaka kansa bayan tarwatsa kansa da boma bomai yayin samamen da dakarun musamman na Amurka suka kai arewa maso yammacin Siriya.
342/